Ministan ayyukan gona Jose Pacheco, wanda ya jagoranci wakilan gwamnati wajen tattaunawar ya ce, idan ana tattaunawa dole akwai banbancin ra'ayi, kuma yanzu gwamnati a shirye take ta karbi masu sa ido daga kasashen waje, amma kamar kullum kungiyar Renamo take ba ta da niyyar sassauta nata bukatun.
Shi kuma bangaren kungiyar Renamo ya dage akan sai an yarda da masu sa ido daga kasashen waje da masu shiga tsakani wanda gwamnati ta ki amincewa da su tun farko akan dalilin cewa, abin da za'a tattauna a kai ya shafi harkokin cikin gida ne kawai. (Fatimah)