Bisa labarin da aka bayar, an ce, wadannan hare-hare guda 2 sun auku ne a jihar Sofala, wato inda jam'iyyar adawa ta Renamo ke da rinyaje.
A ranar 21 ga watan Oktobar da ya gabata ne dai sojojin gwamnatin kasar suka kai wani hari ga sansanin sojin jam'iyyar Renamo dake jihar ta Sofala, matakin da ya sanya jam'iyyar ta sanar da jingine yarjejeniyar samar da zaman lafiya da aka daddale, tsakaninta da gwamnatin kasar a shekarar 1992.
Rahotanni sun bayyana cewa a makwanni biyun da suka gabata, dakaru dauke da makamai na jam'iyyar ta Renamo, sun kai hare-hare ga sojoji da fararen hula har sau da dama.(Bako)