Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Putin da Trump da Sarki Salman sun amince da yarjejeniyar OPEC ta rage yawan man da ake samarwa
2020-04-13 10:39:23        cri
Shugaban Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na Amurka Donald Trump da Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, sun amince da yarjejeniyar da kungiyar kasashe masu fitar da man fetur OPEC ta cimma, na rage yawan man da ake samarwa.

Wata sanarwa da ofishin yada labarai na fadar Kremlin ta Rasha ya fitar, ta ce Shugaba Putin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump da Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz bin Al Saud.

Sanarwar ta ce, shugabannin sun amince da yarjejeniyar da kungiyar OPEC da sauran kasashe masu fitar da mai suka cimma na rage yawan man da ake samarwa da nufin daidaita kasuwar mai ta duniya da tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arzikin duniya.

Kasashen OPEC da sauran kasashe masu fitar da mai karkashin Rasha, sun cimma matsayar ne a jiya Lahadi bayan shafe kwanaki 4 ana tattaunawa, inda suka amince da rage man da ake samarwa da ganga miliyan 9.7 tsakanin watannin Mayu da Yuni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China