Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin mai na kasar Sin ya gano sama da tan biliyan 1.8 na fetur da iskar gas a shekarar 2019
2020-01-02 11:19:46        cri
Kamfanin man fetur na kasar Sin, katafaren kamfanin mai da iskar gas na kasar, ya yi nasarar gano tan biliyan 1.84 na fetur da iskar gas dake kwance a karkashin a shekarar 2019.

A cewar kamfanin, an gano sama da tan biliyan 1 na mai ne a kwarin Ordos, yayin da aka gano sama da cubic mita tirilyan 1 na gas a kwarin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin da kuma kwarin Tarim dake arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin ya danganta wannan sakamako ne ga managartan matakan hakowa da fashohin kirkire-kirkire da aka yi amfani da su. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China