Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mambobin OPEC sun amince da ci gaba da rage danyen mai da suke fitarwa har zuwa watan Disamba
2019-09-13 16:25:34        cri
A jiya Alhamis ne kasashe mambobin kungiyar OPEC, suka amince da ci gaba da rage yawan danyen mai da suke fitarwa zuwa watan Disamban karshen shekara.

Yayin taron kungiyar na 16 da ya gudana a birnin Abu Dhabi fadar mulkin hadaddiyar daular larabawa, kwamitin ministoci mai aikin sanya ido na kungiyar ko JMMC a takaice, ya amince da daukar wannan mataki.

Yayin taron, kasar Saudiyya ta ce za ta daidaita yawan man da take fitarwa zuwa ganga miliyan 9.89 a ko wace rana, daga watan Oktoba mai zuwa, yayin da kasashen Iraqi da Najeriya suka amince da kara rage yawan man da suke fitarwa.

Cikin wata sanarwa da kwamitin na JMMC ya fitar, ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da matakan hadin gwiwa, a fannin daidaita farashin danyen mai a kasuwannin duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China