Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gabatar da sabon jadawalin ayyukan sararin samaniya
2019-12-13 11:15:37        cri

A jiya Alhamis, yayin wani taron jami'ar koyar da fasahohin jiragen sama ta birnin Beijing, babban manajan kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin Yuan Jie, ya yi bayani kan manyan shirye-shiryen da kamfanin zai fara aiwatarwa a nan gaba.

Ya ce, a shekarar 2020 mai zuwa, manyan shirye-shiryen da kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na Sin zai gudanar za su hada da, tashar sararin samaniya mai dauke da dan Adam dake kusa da kasa, wadda za ta samu kulawa cikin dogon lokaci, da dawowa daga duniyar wata bayan bincike, da tsarin tauraron dan Adam na Beidou dake ba da jagoranci kan zirga-zirga na duniya, da shirin sauka da yin bincike a duniyar Mars karo na farko da dai sauransu.

Ya ce ya zuwa shekarar 2030, kamfanin zai gudanar da shirin dawowa daga duniyar Mars bayan bincike, da shirin yin bincike kan duniyoyin dake kewayen rana, wadanda mutane za su iya rayuwa a cikinsu da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China