![]() |
|
2019-10-11 10:59:37 cri |
Yayin wani taron manema labarai, shugaban sashen kula da ilimin gaba da sakandare na ma'aikatar, Wu Yan, ya ce hukumar kula da harkokin kudi ta kasar Sin, ta ware yuan miliyan 889, kwatankwacin dala miliyan 124, domin gina cibiyoyin bada horo a kwalejoji da jami'o'in kasar 19, da nufin inganta gyare-gyare a fannin bada ilimin kasuwanci da kirkire kirkire.
Ya ce yanzu haka, akwai kwasakwasai 28,000 na kirkire kirkire da kasuwanci na intanet da wadanda ba na intanta ba, a fadin kasar. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China