Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani game da gina birnin Shenzhen
2019-08-29 08:29:50        cri

A kwanakin baya ne kwamitin kolin JKS, da majalissar gudanarwar kasar suka fitar da takardun bayanai, dake nuna cewa, za a gina birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, ta yadda zai zama yankin gwaji na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin mai matukar kayatarwa.

Takardun bayanan wadanda ta kuma nuna cewa, gina wannan yanki zai taimaka wajen kara aiwatar da manufofin zurfafa gyare gyare, da kara bude kofa ga waje daga dukkanin fannoni.

Aikin zai kuma tallafa wajen cimma nasarar aiwatar da manufar gina yankin Guangdong zuwa Hong Kong zuwa Macao, tare da alamta cimma burin kasar Sin na zama kasa wadda ke farfadowa.

Takardun bayanan sun kara da cewa, nan da shekarar 2025, Shenzhen zai zama daya daga manyan birane a duniya a fannin bunkasar tattalin arziki da ingancin ci gaba. Kaza lika tsarin birnin na bincike da bunkasuwa, da nagartar masana'antu, da fadadar kirkire kirkiren sa, tare da kyautatar hidimomin al'umma, da ma kyakkyawan yanayin muhallin halittun birnin, duka za su zamo a sahun gaba a duniya.

Haka kuma, nan da shekarar 2035, birnin zai zamo a sahun gaba a fannin karfin takarar tattalin arziki, da kirkiro sabbin fasahohin zamani, da sabbin hanyoyin neman ci gaba a fadin duniya. Bugu da kari, ya zuwa karshen karnin da muke ciki yanzu, birnin Shenzhen zai kasance birni mafi shahara kuma abin koyi ga sauran biranen duniya, a fannonin samun karfin takara da kirkiro sabbin abubuwan zamani.(Ahmed, Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China