Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gano sabuwar rijiyar hakar mai a tekun Bohai na kasar Sin
2020-03-19 13:11:03        cri

Kamfanin samar da man fetur daga tekuna na kasar Sin, ya sanar a jiya cewa, an gano sabuwar rijiyar hakar mai, a wurin hakar mai dake tekun Bohai na kasar Sin, an kuma gano wannan rijiyar ne a arewacin mashigin teku na Laizhou na tekun Bohai, kuma tsayin wurin dake da mai a rijiyar ya kai kimanin mita 20.

An yi bayanin cewa, yawan mai da za a samar a wurin zai kai ganguna fiye da dubu 400, wanda zai iya biya bukatun kananan motoci dubu 10 da za su yi tafiya har ta tsawon shekaru 5.

Yawan man da aka gano a cikin rijiyar yana da yawa, kana man da za'a haka yana da inganci. Kana wannan ya kawar da yanayin rashin samun mai domin amfani na ciniki a wannan wuri har na tsawon shekaru fiye da 40, kuma an shaida kyakkyawar makomar hakar mai a yankin kudancin tekun Bohai, wanda ya aza tubali, don cimma burin samar da mai har ton miliyan 40, har na tsawon shekaru 10 a wurin. Kuma yana da babbar ma'ana wajen tabbatar da tsaron makamashin kasar, da kiyaye samar da mai a gabashin kasar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China