Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun samar da dala miliyan 141 ga asusun wanzar da zaman lafiyar nahiyar
2020-01-14 21:01:51        cri
Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya ce daga shekarar 2017 kawo yanzu, kasashen Afirka sun samar da kudaden da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 141, ga asusun nahiyar na wanzar da zaman lafiya.

Moussa Faki Mahamat ya bayyana hakan ne a yau Talatar. Ya ce matakin ya tabbatar da irin gagarumin ci gaba da aka samu, game da kokarin cimma nasarar kudurorin tsayawar nahiyar da kafafunta ta fuskar kudaden gudanar da ayyuka, wadanda majalissar gudanarwar kungiyar ta amincewa a shekarar 2015.

Jami'in ya kara da cewa, yawan kudaden tallafin da kasashen Afirka suka tara, ya nuna jajircewer kasashe mambobin kungiyar ta AU, wajen samar da kudaden da ake bukata, yayin ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China