Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yayin da farashin mai ya fadi a kasuwar duniya, manyan kasashe masu samar da mai a Afrika sun yi gargadi game da shiga mawuyacin yanayi a nan gaba
2020-03-13 12:00:33        cri
Kasashen Nijeriya da Angola, mambobin kungiyar OPEC, ta kasashe masu samar da man fetur, kuma kasashe biyu mafi samar da danyen man fetur a nahiyar Afrika, sun yi gargadi game da shiga mawuyacin hali cikin watanni masu zuwa, biyo bayan faduwar farashin man a duniya, a farkon makon nan.

Mele Kyari, shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC, ya bayyana a ranar Laraba cewa, kasar mafi karfin tattalin arziki a Afrika, ta fara ganin tasirin faduwar farashin, yana mai cewa, idan kasuwar mai ta rushe, to komai zai rushe, musammam a kasa kamar Nijeriya da ta dogara da man fetur.

Ita ma Angola, kasa ta biyu mafi fitar da man fetur bayan Nijeriya, na fuskantar kalubale, inda bangaren man ya gamu da tasgaro.

Hukumar samar da man fetur da iskar gas da makamashi mai tsafta ta Angola, ta ce har yanzu tana nazari kan tasirin faduwar farashin man a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China