Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin baje kolin CIIE zai samar da sabbin damammaki na ciniki, in ji EU
2019-11-04 19:13:59        cri
Kwanan baya, wakilin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU ya sanar da cewa, kungiyar EU tana maraba ga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wanda ya samar da sabbin damammaki ta fuskar ciniki ga mambobin kungiyar EU da kamfanonin kungiyar.

Dangane da wannan harka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin tana da imanin cewa, tabbas kasashe da kamfanonin Turai, wadanda za su halarci bikin za su samu gamsuwa.

Geng Shuang ya kuma jaddada cewa, kasar Sin da kungiyar EU su ne masu samun ci gaba a fannin tattalin arziki a duk duniya, sun kuma cimma matsayi daya kan harkokin kiyaye cinikin dake tsakanin kasa da kasa, da kuma ciniki mai bude kofa ga waje, kana dukkansu suna adawa da kariyar ciniki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China