Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an kasashen waje sun ce baje kolin CIIE zai kara zurfafa hadin gwiwar Sin da kasashen duniya
2019-11-03 16:38:39        cri
Wasu jami'an kasashen waje sun bayyana cewa bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu wato (CIIE) a birnin Shanghai, wanba za'a gudanar daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, wata muhimmiyar dama ce ga kasashen duniya, inda za su kara zurfafa hadin gwiwarsu da kasar Sin.

Firaiministan kasar Girka, Kyriakos Mitsotakis ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua yayin wata tattaunawa da suka yi kwanan nan cewa, bajekolin CIIE karo ba biyu ya kasance wani muhimmin dandali na kara karfafa dangantaka tsakanin Girka da Sin duk da yiwuwar rashin tabbas game da harkokin duniya a nan gaba.

Shi kuwa Sanny Ntayombya, shugaban sashen sadarwa da kasuwanci na hukumar bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar Rwanda, ya yabawa bikin baje kolin, inda ya bayyana shi da cewa wata muhimmiyar dama ce wadda Rwanda za ta samu damar shigar da kayayyakinta a kasuwannin kasar Sin.

Nomalungelo Gina, mataimakin ministan ciniki da bunkasa tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu, ya ce wannan bikin baje kolin zai baiwa kamfanonin kasar Afrika ta kudu damar samun wasu karin hanyoyin shigar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin kasar Sin.

Sama da kamfanoni 3,000 daga kasashen duniya da yankuna 150 ne suka nuna sha'awarsu ta shiga baje kolin CIIE na bana, wanda ya hada har da wasu manyan kamfanonin duniya 250. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China