Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin zata bunkasa shirin wayar da kan mazauna yankunan karkara
2019-10-30 11:08:57        cri

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu ka'idoji game da yunkurin hukumomin kasar na kara kawar da gurbatattun al'adu da kuma kara wayar da kan al'umma mazauna yankunan karkara.

Duk da irin cigaban da aka samu a 'yan shekarun baya bayan nan, wasu matsaloli da suka hada da almubazzaranci da dukiyoyi a lokutan bikin binne mamata, da wasu munanan al'adu da kuma yadda ake kin kula da tsofafi har yanzu yana cigaba da wanzuwa. Za'a gudanar da cikakken kokari wajen mutunta al'adun gargajiyar yankunan, kana za'a yi la'akari da irin zabin da jama'a keda shi, sannan za'a yi watsi da daukar duk wasu tsauraran matakai wajen daidaita al'amurra. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China