Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar da wasu kasashe ciki hadda Amurka suka yi
2019-10-30 14:25:04        cri

Game da kalamomi maras tushe da wasu kasashe ciki hadda Amurka suka yi kan batun yankin Xinjiang na kasar Sin a gun taron MDD, zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya yi Allah wadai da al'amarin cikin kakkausar murya.

Zhang Jun ya jaddada cewa, Amurka ta yi suka kan kasar Sin ba tare da wani shaida ba, lamarin da ya zama shisshigi cikin harkokin gidan kasar, da tayar da tankiya kan kasar Sin, yana mai bayyana rashin jin dadin Sin da cewa, ba za ta yarda da hakan ba ko kadan. Matakin da Sin take dauka kan Xinjiang wajen kawar da tsattsauran ra'ayi da dakile ta'addanci na bisa nazarin da aka yi, wanda ya biya bukatar jama'a, kuma bai kasance batun keta hakkin Bil Adama ba, balle ra'ayin bambancin kabilu. Jama'ar duniya sun san gaskiya, kuma sun fahimci hakikanin halin da ake ciki yanzu. Sin na yin kira ga wasu kasashe, kada su yi tankiya da al'ummar duniya, da bin hanyar da ba ta dace ba. Kuma ba wanda zai hana ci gaban zaman al'ummar Sinawa, sa'an nan kasar Sin na da makoma mai haske, in ji jami'in na kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China