Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNCTAD za ta tura tawaga zuwa baje kolin CIIE
2019-11-04 13:12:10        cri

Hukumar raya kasuwanci da bunkasa ci gaba ta MDD (UNCTAD), mai helkwata a Geneva, ta kasar Switzerland, za ta tura tawagar wakilai don halartar bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) karo na 2. Kafin tashinsa, babban sakataren hukumar UNCTAD Mukhisa Kituyi, ya gudanar da tattaunawa da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin kasar Sin CMG. Ya ce, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin ya samar da sabuwar dama ga kasashen dake da sha'awar shigo da kayayyakinsu kasuwannin kasar Sin da kuma kawo ci gaba ga duniya.

Mukhisa Kituyi ya ce, akwai kasashe masu yawa da za su shiga baje kolin na wannan shekarar, a cewarsa, hakan ya nuna cewa, baje kolin da aka gudanar na shekarar da ta gabata ya samu gagarumar nasara. Kasar Sin ta samar da muhimmiyar dama ta ba da kwarin gwiwa ga kasashe masu tasowa. A daidai lokacin da duniya ke fuskantar rashin tabbas da kokarin haifar da kariyar ciniki, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin muhimmiyar dama ce, musamman ga kasashe masu tasowa.

Mukhisa Kituyi ya ce, damar da kasar Sin ta bayar ta bude kofa ga kasashen duniya ta nuna cewa, makomar dangantakar kasa da kasa ta dogara ne kan mu'amalar girmama juna, a maimakon kafa shinge a tsarin mu'amalar ciniki. Kasar Sin ta jima tana gudanar da tsarin mu'amalar cinikayya na bangarori daban daban, wanda hakan shi ne hanyar da ta dace da duniya ta bi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China