Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tanzania za ta inganta cinikayya yayin taron CIIE
2019-11-02 16:08:16        cri

Hukumomi a Tanzania, sun ce kasar ta gabashin Afrika, na sa ran inganta harkokinta na cinikayya yayin taron baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2 da zai gudana a Shanghai.

Ministan kula da masana'antu da ciniyayya na kasar, Innocent Bashungwa, ya shaidawa Xinhua cewa, baje koli zai zama wurin da Tanzania za ta gabatar da abubuwan da za ta iya cinikayyarsu da kasar Sin da sauran kasashen da za su hallara.

Innocent Bashungwa, wanda zai jagoranci tawagar kasar zuwa taron baje kolin, ya ce taron zai ba kasar damar tallata damarmakin zuba jari da take da su a bangarorin aikin gona da hakar ma'adinai da kiwon kifi.

Ya ce Tanzania ta amfana daga baje kolin na farko da aka yi a bara, inda ta samu karin adadin masu zuwa yawon bude ido daga kasar Sin.

Kididdiga ta nuna cewa, kimanin Sinawa masu yawon bude ido 30,000 ne suka ziyarci Tanzania a bara.

Ministan ya kara da cewa, kasar Sin na kara bude kofar cinikayya ga sauran sassan duniya, yana mai cewa, baje kolin dake tafe, na daya daga cikin hanyoyin da kasar ke bude kofarta da kara harkokin cinikayya a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China