Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni sama da dubu 3 za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2
2019-11-01 12:39:43        cri

A halin yanzu, kamfanoni sama da dubu 3 daga kasashe da yankuna sama da 150 za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 2, kuma cikinsu akwai kamfanonin kasashen waje fiye da dubu 1 wadanda za su halarci bikin karo na farko. Bugu da kari, kamfanoni da dama za su kawo nagartattun kayayyakinsu zuwa wannan biki.

Idan aka kwatanta da bikin na bara, a bana, fadin yankunan nune-nune da adadin kayayyakin da za a nuna, da kuma yawan kamfanonin da za su halarci biki, dukkansu sun karu. A fannin fadin yankunan nune-nune, ya karu zuwa murabba'in mita dubu 300 daga murabba'in mita dubu 270 na shekarar 2018. Sa'an nan, a fannin karfin kamfanonin dake halartar bikin kuma, a shekarar 2018, kamfanoni 220 dake cikin jerin manyan kamfanonin kasa da kasa guda dari 5, sun halarci bikin, a bana ma, adadin ya karu zuwa 250. Bugu da kari, bisa hasashen da aka yi, adadin sabbin kayayyaki da fasahohin da za a nuna a biki na bana, zai wuce na bikin karo na farko. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China