in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mene ne bambancin da ke tsakanin cututtukan mura da Flu da COVID-19?
2020-03-24 13:14:34 cri

Masu karatu, yanzu an samu barkwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a sassan duniya. Kuma mutane na tsoron kamuwa da annobar. To mene ne bambancin da ke tsakanin cututtukan mura, Flu da COVID-19? Yau mun gayyaci Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing a zaurenmu, za kuma ta yi muku karin bayani kan bambancin da ke tsakanin cututtukan mura, Flu da COVID-19.

Cutar mura, wani nau'in cuta ce da a kan kamu da ita yayin da aka gaji, ko aka ji sanyi. Alamomin da ake da su sakamakon kamuwa da cutar sun hada da toshewar hanci, majina a hanci, yin atishawa. Ba a yin zazzabi kuma ba a karancin karfin jiki. Haka kuma ba a ji ciwon kai, gabbai, da ma duk jiki baki daya. A yawancin lokaci, cutar murar ba ta kawo wa mutane hadari sosai ba, ba ta Yaduwa tsakanin mutane.

Annobar cutar Influenza, wani nau'in cuta ce wadda ke saurin yaduwa tsakanin yawan mutane sakamakon kwayoyin cutar iri 3 wato A,B,da C. Annobar tana yaduwa ne ta hanyar yawu ko majina da suka bi iska, ko mu'amala da mai dauke da ita ko kuma taba wani abu da kwayar cutar ta taba. Idan wani ya kamu da annobar, ya kan ji alamu masu tsanani cikin sauri, kamar zazzabi har zafin jiki ya wuce digiri 39 cikin kwana guda, ciwon kai, rashin karfin jiki, da rashin son cin abinci. Annobar cutar ta Influenza ta kan yadu a lokacin sanyi da lokacin bazara. A kan yi fama da munanan cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da annobar, har ma wasu su kan rasa rayukansu, musamman ma tsoffafi, kananan yara, masu juna biyu da marasa lafiya da ke doguwar jiyya.

Ruwa da miyau dake fitowa daga hanci da baki da kuma mu'amala da jama'a, su ne manyan hanyoyin yada annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ana hasashen cewa, ana iya yada cutar yayin da aka sha ruwa ko shafi gurbatacciyar iska, sakamakon shigar najasar da ke dauke da kwayoyin cutar cikin iskar ko ruwan. Ban da wannan kuma akwai yiwuwar yada cutar ta hanyar iska wato yayin da aka yi tari ko atishawa da ke dauke da kwayoyin cuta.

Idan wani mutum ya kamu da annobar, zai rika jin alamomin zazzabi, rashin karfin jiki, da tari. Ba safai a kan yi fama da toshewar hanci da majina a hanci ba. Yawancin wadanda annobar ta harba su kan warke daga annobar cikin sauri kuma ba su cikin hali mai tsanani. Amma tsofaffi da marasa lafiya da ke doguwar jiyya su kan fuskanci babbar barazana. Hakika mafi yawancin wadanda suka kamu da annobar a kan sallame su daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga cutar.

Wannan shi ne bambancin da ke tsakanin cutar mura da annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19. Ta yaya zamu yaki cutar idan ba mu taki sa'a ba, mun kamu da su? Zhang Chuji, wata likita dake aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba mu kyakkyawar shawara, inda ta ce, cutar mura, annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19, dukkan su cututtuka ne da masu kamuwa da cutar suke fi dogaro da karfin jikinsu na yaki da cutar, idan cututtukan ba su yi kamari ba, wadanda suka kamu su huta sosai a gida, su kwanta a kan gada, su kebe kansu daga iyalansu da abokansu, su sha ruwa da yawa, sun ci abinci mai ruwa-ruwa masu gina jiki. Bayan sun ci abinci, su wanke baki da ruwa mai dumi ko kuma ruwan gishiri mai dumi. A rika kuma wanke hannu a kai a kai. Kada a taba ido da hanci da baki da hannaye masu kazanta. Amma idan cutar ta yi kamari, ko kuma an kamu da cututtukan da suke biyo bayan kamuwa da cutar ta mura da annobar cutar Influenza da kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19, to ya zama tilas a je asibiti nan take ba tare da bata lokaci ba don ganin likita da samun jiyya yadda ya kamata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China