in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin kitse da yawa, gami da wasu sinadarai na iya yin illa ga jijiyoyin jini
2020-03-03 09:30:00 cri

Cin nau' in abinci na Ketogenic-diet, ko kuma KD a takaice, wato abinci mai fitar da kitse da yawa, sinadaran gina jiki da na kara kuzari kalilan. Wasu wadanda suke kokarin rage kiba suna sha'awar cin irin wannan nau'in abinci na KD. Duk da haka wani sabon nazari da aka kaddamar a mujallar "sinadaran gina jiki" ta kasa da kasa ya nuna mana cewa, idan mutum ya ci kitse da yawa na gajeren lokaci, sinadaran gina jiki kadan amma nisadaran kara kuzari kalilan, nan da nan kuma ya dawo tsarin cin abinci yadda ya kamata, hakan na iya raunana jijjiyoyin jininsa cikin sauki.

Masu nazari sun gudanar da nazarinsu kan maza 9 masu koshin lafiya, inda suka bukace su ci abinci bisa salon na KD na kwanaki 7, sa'an nan su sha ruwa mai cike da sukari giram 75. Salon KD da wadannan maza 9 suka bi, yana samun karbuwa sosai a halin yanzu, inda suka ci kitsen da yawansa ya kai kaso 70 na jimillar abincinsu, da kaso 10 na sinadaran kara kuzari da kuma kaso 20 na sinadaran gina jiki.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, wasu jijjiyoyin jini a jikin wadannan maza sun gamu da matsala. Masu nazarin suna ganin cewa, babban dalilin da ya sa haka shi ne domin cin abinci bisa salon KD cikin gajeren lokaci yana kawo illa ga daidaiton yawan sukari da ke jikin mutum, idan sun dawo da tsarin cin abincinsu kamar yadda suke yi a baya, sun kuma ci isassun sinadaran kara kuzari yadda ya kamata, yawan sukari da ke cikin jininsu zai karu cikin sauri, sa'an nan jikinsu zai sarrafa sinadarai sosai, ta haka jijjiyoyin jininsu za su sarrafa tsoffin kwayoyin halitta. Idan mutanen da suke fuskantar babbar barazanar kamuwa da cututtukan jijjiyoyin jinin zuciya sun ci abinci bisa salon KD, yawan sukari da ke cikin jininsu zai karu cikin sauri, kuma hakan zai iya illata jijjiyoyin jininsu sosai.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, dukkan wadanda aka gudanar da nazarin, maza ne kuma ba su da yawa. Nan gaba za a gudanar da karin nazari don tabbatar da sakamakon nazarin.

Wasu kan ce, cin abinci bisa salon na KD wato cin kitse da yawa, sinadaran gina jiki kadan amma sinadaran kara kuzari kalilan, yana iya barin jikin dan Adam ya yi amfani da kitsen da ke jikin a maimakon sukarin da ke cikin jikin. Amma wasu kwararru suna ganin cewa, cin abinci bisa salon na KD cikin dogon lokaci yana iya yin barazana ga lafiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China