in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsoffi masu koshin lafiya ba su bukatar shan maganin Aspirin a ko wace rana
2020-02-02 15:28:03 cri

Wasu na ganin cewa, shan maganin Aspirin yana iya taimakawa tsoffafi su rage barazanar kamuwa da cututtukan jijjiyoyin jinin zuciya. Duk da haka wani nazari da aka gudanar cikin dimbin mutane ya nuna mana cewa, ana bukatar tabbatar da amfanin maganin na Aspirin, sa'an nan kamata ya yi a yi taka tsan-tsan kan illolin da aka samu sakamakon shan maganin cikin dogon lokaci.

Masu nazari daga kasar Australia sun kaddamar da rahoton nazari a kwanan baya cewa, sun dauki shekaru 7 suna gudanar da nazarinsu kan tsoffafi masu koshin lafiya fiye da dubu 19 wadanda shekarunsu suka zarce 70 da haihuwa, a kokarin tabbatar da cewa, ko shan maganin Aspirin a ko wace rana zai iya yin rigakafin kamuwa da cututtukan jijjiyoyin jinin zuciya ko a'a.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, shan maganin Aspirin a ko wace rana ba zai iya raga barazanar barkewar ciwon zuciya ko kuma kamuwa da shan inna da yawa ba, haka kuma ba zai iya tsawaita tsawon rayuwar mutane ba. Ban da haka kuma, mutanen da yawansu ya kai kaso 3.8 bisa jimillar wadanda suke shan maganin sun yi fama da fid da jini kwarai, yayin da adadin ya kai kaso 2.8 kawai cikin wadanda suka sha wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki, a kan bai wa mutane a lokacin da ake gwajin amfanin maganin a Aspirin. Shan maganin Aspirin kan haifar da fitar jinni daga kayayyakin ciki masu narka abinci, musamman ma tsakanin tsoffafi.

Masu nazarin daga jami'ar Monash ta kasar Australia sun yi karin bayani da cewa, nazarin da suka gudanar tsakanin dimbin mutane sun shaida cewa, tsoffafi masu koshin lafiya ba su bukatar shan maganin na Aspirin. Amma duk da haka kamata ya yi wadanda suke fama da ciwon zuciya da shan inna su sha maganin bisa iznin likita.

Masu nazarin sun jaddada cewa, maganin na Aspirin, wani nau'in magani ne mai inganci. Amma ana bukatar ci gaba da nazari kan amfanin maganin da kuma barazanarsa idan an dauki tsawon lokacin ana sha. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China