in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon nazari ya bayyana barazanar da abincin da aka sarrafa su sosai suke kawo wa lafiyar mutane
2020-03-03 09:31:22 cri

Yanzu abincin da aka sarrafa su sosai sun kasance tamkar abincin yau da kullum ga dimbin mutane. Amma wasu nazarce-nazarce guda 2 da aka kaddamar cikin sabon "mujallar ilmin likitancin kasar Birtaniya" sun nuna mana cewa, kamuwa da cututtukan jijjiyoyin zuciya da kwakwalwa da kuma mutuwa da wuri, suna da nasaba da cin abincin da aka sarrafa su sosai. Wannan sakamako ya tabbatar da sakamakon nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya, wato abincin da aka sarrafa su sosai kan kawo barazana ga lafiya.

An yi karin bayani da cewa, abincin da aka sarrafa su sosai sun hada da gasassun abinci da biskit wadanda aka kunshe a cikin wani abu, lemun kwalba, abincin da ake kara musu sinadare a ciki domin kara masa dadi ko adanawa, miyar da aka sarrafa tare da busassun kayayyakin lambu da dai sauransu. Kullum suna kunshe da sukari mai yawa, kitse, gishiri, amma ba su da isassun sinadaran bitamin da fiber. A wasu kasashe, yawan abincin da aka sarrafa su sosai wadanda mutane suke ci ya kai kaso 25 zuwa 60 bisa jimillar abincin da ake ci a zaman yau da kullum.

Masu nazari daga kasar Faransa sun sake bibiyar lafiyar mutane fiye da dubu 100 da kuma yadda suka ci abinci daga shekarar 2009 zuwa 2018. Sun gano cewa, abincin da aka sarrafa su sosai suna iya haddasa barazana a wasu fannoni. Alal misali, idan yawan abincin da aka sarrafa su sosai wadanda aka ci a zaman yau da kullum ya karu da kaso 10, to barazanar kamuwa da cututtukan jijjiyoyin zuciya za ta karu da kaso 12, kana barazanar kamuwa da cututtukan jijjiyoyin kwakwalwa za ta karu da kaso 11.

Masu nazari daga kasar Safaniya sun sake bibiyar halin da matasa dubu 20 da suka gama karatu daga jami'a suka kasance daga shekarar 1999 zuwa 2014. Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, kwatankwacin wadanda suka ci abincin da aka sarrafa su sosai sau daya ko biyu a ko wace rana, wadanda suka ci abincin da aka sarrafa su sosai fiye da sau hudu a ko wace rana sun fi fuskantar barazanar mutuwa har kashi 62 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, a baya an gudanar da nazari ne don gano alakar da ke tsakanin abincin da aka sarrafa su sosai, da matsalar kiba, ciwon hawan jini, da wasu cututtukan sankara. Sai dai sabbin nazarce-nazarce guda 2 sun kara tabbatar da sakamakon wadannan nazarce-nazarce. Amma duk da haka, akwai bukatar ci gaba da nazari don gano dalilin da ya sa cin abincin da aka sarrafa su sosai da yawa yake kawo barazana ga lafiyar mutane. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China