in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abincin ganye bai amfanawa wa kwakwalwar mutane
2020-03-03 09:32:38 cri

Ko da yake ana kira da a rika cin abincin ganye don kiyaye muhallin duniyarmu, amma masana ilmin abubuwa masu gina jiki sun yi nuni da cewa, watakila cin abincin ganye yana hana sinadarin choline shiga cikin jikin dan-Adam, wanda yake da matukar muhimmanci ga kwakwalwa

Masana ilmin abubuwa masu gina jiki sun yi kira da cewa, kamata ya yi masu aikin kula da lafiyar mutane da kuma masu sayayya su kara fahimtar muhimmancin cin abinci masu cike da sinadarin choline da kuma yadda wannan sinadarin zai shiga cikin jiki. Idan babu isasshen sinadarin na choline a jiki kamar yadda aka ba da shawara, to, dole ne a ci abinci masu cike da sinadarin ko kuma a shan maganin sinadarin, musamman ma yadda masu juna biyu suke bukatar isasshen sinadarin na choline a jikinsu, saboda yana da muhimmanci kwarai da gaske ga 'yan tayinsu.

Masu nazari sun kaddamar da bayaninsu a kwanan baya cewa, a kan samu sinadarin na choline ne a cikin abincin dabbobi, wanda yake amfanawa lafiyar kwakwalwar mutane, musamman ma kwakwalwar 'yan tayi, kana kuma yana da amfani ga hantar bil-Adam. Amma idan hanta ba ta iya samar da isasshen sinadarin na choline, akwai bukatar shigar da sinadarin ta hanyar cin abinci da shan magani.

A kan samu sinadarin na choline ne daga naman sa, kwai, abincin madara, kifi da naman kaji, har ila yau kuma akwai sinadarin kalilan a cikin dangin gyada, wake, broccoli da dai sauransu. Yanzu wasu littattafai dake bayanai kan nau'o'in abinci na yau da kullum sun yi kira da a rage shan madara, da cin kwai da abinci masu cike da abincin dabbobi, watakila hakan zai hana samun isasshen sinadarin na choline.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, tun daga shekarar 1998 kwalejin nazarin ilmin likitanci na kasar Amurka ya ba da shawarar cewa, kamata ya yi mata su samu choline da yawansa ya kai miligiram a kalla 425 a ko wace rana, yayin da ake son maza su samu sinadarin da yawansa ya kai miligiram a kalla 550 a ko wace rana. Haka kuma, masu juna biyu da kuma matan da suke shayarwa suna bukatar sinadarin da yawansa ya kai miligiram 450 da kuma miligiram 550 a ko wace rana. A shekarar 2016, hukumar kula da ingancin abinci ta kungiyar tarayyar Turai ta ba da shawara kan yawan sinadarin na choline da ya fi kyau mutane su samu a ko wace rana. Amma sakamakon nazari da aka gudanar kan yadda ake cin abinci a kasashen arewacin Amurka, Australia da Turai ya nuna mana cewa, yawan sinadarin choline da ake samu a ko wace rana ya yi kasa da yadda aka ba da shawara. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China