in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ta yaya muke kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19?
2020-03-03 09:36:07 cri

Ranar Jumma'a 28 ga wata, Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Nijeriya ta tabbatar da wani mutum da ya kamu da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a jihar Lagos a ranar 27 ga wata, wanda shi ne na farko da aka tabbatar ya kamu da annobar a Nijeriya tun bayan barkewar annobar a kasar Sin a watan Janairun bana.

Dan kasar Italiya da ya kamu da cutar, yana aiki ne a Nijeriya, ya koma Lagos daga birnin Milan na Italiya a ranar 25 ga wata. Dakin gwaje-gwaje na sashen nazarin kwayoyin cuta na asibitin jami'ar Lagos ya tabbatar da cewa, mutumin ya kamu da annobar. Yanzu haka yana samun jiyya a asibitin shawo kan cututtuka masu yaduwa a Yaba da ke Lagos, kuma ba ya cikin hali mai tsanani.

Gwamnatin Nijeriya tana inganta matakanta na kandagarki da dakile yaduwar annobar. Cibiyar kandagarki da hana yaduwar annoba ta Nijeriya NCDC tana jagorantar hukumomin yaki da cutar COVID-19 wajen daukar matakan gaggawa, za kuma ta hada kai da hukumar lafiya ta Lagos don daidaita barkewar annobar da kuma daukar matakai. Ma'aikatar lafiyar Nijeriya ta kuma yi gargadin cewa, a daina yada jita-jita da za su tsorata mutane a kan Internet. Ma'aikatar za ta ci gaba da ba da labaru da dumi-duminsu da kuma daukar dukkan matakan da suka wajaba,a kokarin hana barkewar annobar a kasar.

Ruwa da miyau dake fitowa daga hanci da baki da kuma mu'amala da jama'a, su ne manyan hanyoyin yada cutar COVID-19. Ana hasashen cewa, ana iya yada cutar ce yayin da aka sha ruwa ko shafi gurbatacciyar iska, sakamakon shigar najasar da ke dauke da kwayoyin cutar cikin iskar ko ruwan. Ban da wannan kuma akwai yiwuwar yada cutar ta hanyar iska wato yayin da aka yi tari ko atishawa da ke dauke da kwayoyin cuta."

Idan mutum ya kamu da annobar, zai rika jin alamomi na yi zazzabi, rashin karfin jiki, da tari. Ba safai a kan yi fama da toshewar hanci da majina a hanci ba. Yawancin wadanda annobar ta harba su kan warke daga annobar cikin sauri kuma ba su cikin hali mai tsanani. Amma tsofaffi da marasa lafiya da ke doguwar jiyya su kan fuskanci babbar barazana. Hakika mafi yawancin wadanda suka kamu da annobar a kan sallame su daga asibiti bayan an tabbatar sun warke daga cutar.

A yau mun gayyaci Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing inda ta ba mu shawara dangane da matakan kandagarkin annobar. Inda ta ce,

"Ya zama tilas a sanya abun rufi baki da hanci, a rika wanke hannu da ruwa mai tsabta da kuma sabulu a kai a kai, a guji taba ido, baki, da hanci. A nisanci wadanda suke tari ko atishawa a kalla mita 1.5. A tabbatar isa na shiga iska cikin daki a kowa ne lokaci, sa'an nan a guji zuwa wuraren taruwar mutane. Haka zalika kamata ya yi a rufe baki da hanci da takardun goge baki yayin da ake tari ko atishawa, ko kuma a rufe baki da hanci a tsakanin gwiwar hannu a lokacin da ake tari ko atishawa don magance fitar ruwa da miyau daga hanci da baki. "

Har ila yau, ma'aikatar lafiyar Nijeriya ta bukaci cewa, a duk lokacin aka ji alamomi na jin zazzabi, tari, ko matsalar yin numfashi, to a zauna a gida, a buga waya NCDC don samun shawara. Za a iya buga waya a ko da yaushe. Wajibi ne a rika kallo da sauraron kafafen watsa labarai, don kara fahimtar alamomi da matakan magance annobar COVID-19.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China