in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila cin abinci ta hanyar da ba ta dace ba yana sanya kwakwalwar mutane ba ta aiki yadda ya kamata
2020-03-03 09:33:44 cri

Wani sabon nazari da jami'ar kasar Australia ta gudanar ya nuna cewa, yanzu matsakaicin yawan abinci da mutane suke ci a ko wace rana ya fi na shekarun 1970 yawa, kwatankwacin kara cin jerin abincin da aka shirya tare da burodin da aka kunsa nama da ganye a cikinsa wato hamburger. Irin wannan hanyar cin abinci da ba ta dace ba tana sanya kwakwalwar mutane ba ta aiki yadda ya kamata, kana kuma tana iya haddasa kamuwa da ciwon sukari mai nau'i na 2.

Masu nazari daga jami'ar kasar Australia sun bayyana cikin wata sanarwa cewa, mai yiwuwa ne kwakwalwar mutane tana daina aiki da wuri fiye da yadda muke tsammani. Dalilin da ya sa haka shi ne domin a zamanin yau mutane suna rayuwa ta hanyar da ba ta dace ba.

Masu nazarin sun maimaita sakamakon nazarce-nazarcen kasa da kasa guda 200 da aka gudanar a baya, sun kuma sake bibiyar mutane fiye da dubu 7 dangane da lafiyar kwakwalwarsu da yadda suka tsufa. Sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya, inda suka nuna cewa, baligan da yawansu ya kai kashi 30 cikin dari ne a duniya baki daya suke fuskantar matsalar kiba, ko kuma nauyinsu ya wuce misali. Ya zuwa shekarar 2030, baligan da yawansu ya wuce kashi 10 cikin dari ne za su kamu da ciwon sukari mai nau'i na 2. An gano cewa, kwatankwacin shekarun 1970, a zamanin yau mutane suna kara cin hamburger guda, soyayyen dankali da lemun kwalba na kofi kwaf guda a ko wace rana. Abincin da suka ci sun fi yadda suke bukata, ma iya cewa, dimbin mutane suna cin abinci ta hanyar da ba ta dace ba.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, suna da shaida da suka tabbatar da cewa, idan mutane ba su ci abinci ta hanyar da ta dace ba, kana kuma sun dade ba sa motsa jiki yadda ya kamata, za su fuskanci mummunar barazanar kamuwa da ciwon sukari mai nau'i na 2, har ila yau kuma kwakwalwar mutane ba ta aiki yadda ya kamata, alal misali akwai yiwuwar kamuwa da matsalar kaifin basira da shanyewar kwakwalwa. Haka zalika kuma an tabbatar cewa, akwai alaka a tsakanin kamuwa da ciwon sukari mai nau'i na 2 da kuma yadda kwakwalwar mutane ba ta aiki yadda ya kamata.

Masu nazarin sun ci gaba da cewa, kullum yayin da mutane suka zarta shekaru 60 a duniya, a kan ba su shawara dangane da rage barazanar kamuwa da cututtukan kwakwalwa. Amma an makara, wai aikin gama ya gama. Masu nazarin sun jaddada cewa, illolin lafiya da mutane suka gamu da su bayan da suka shiga matsakaitan shekaru na rayuwa, da wahala a magance su. Don haka hanya mafi dacewa ta magance kamuwa da cututtukan kwakwalwa ita ce cin abinci ta hanyar da ta dace da kuma nacewa kan motsa jiki tun ana kuruciya. Masu nazarin sun kuma yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa da masu ilmin likitanci da su taka rawa wajen kare mutane ta hanyar ilimantar da su, don kaucewa cin abinci ta hanyar da ba ta dace ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China