in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rawar da CRI ta taka ga masu sauraro
2017-01-03 08:40:46 cri
Hakika Gidan rediyon kasar sin watau (CRI), ya taka gagarumar rawa ga mu masu sauraro. Tun a watan daya, na shekarar 2016, sashen hausa na CRI, ke cigaba da suburbudo mana, dadadan shirye-shirye, sa suke matukar ilmantarwa, fadakarwa, dama nishadantar da mu masu sauraro. Ta hanyar kayatattun shiraruwa, tun daga farkon mako, har izuwa, karshen mako, kama daga, shafa labari shuni, Kade-kaden africa, Zabi Sonka, da bamu damar sadar da zumunci, Wasikun masu sauraro, Koyon sinanci, da sauran dinbin shiraruwa. Wanda sun ilmantar damu matuka, tare ilmantar damu, duk a shekarar da ke karewa ne, wakilin CRI a najeriya Murtala Zhang, ya kammala aikin sa, ya koma Sin, wanda mukayi matukar kewarsa, ganin yanda yake sadar da zumunta, ta hanyar kiran mu masu sauraro CRI.

A gefe daya, muke jimamin na kammala aiki da kwararrun 'yan jarida sukai, da CRI, Fatima Jibril, Mamman Ada, wanda muke masu fatan Alkhairi, a duk yanayin da suka tsinci kansu.

Daga Karshe nake kara jinjina ga sashen hausa na CRI, bisa kokarin ma'aikatan sa, na hulda da mu ma'abota sauraren sa.

Daga Aminu Dankaduna Amanawa, Jihar Sokoto a Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China