in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasikar nuna murna tare da kara goyan baya ga sashen Hausa na CRI
2016-12-23 15:01:55 cri

Zuwa ga Malama Fatima Liu sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin maaikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya. Bayan haka dalilin rubuto muku wannan sako domin naji dadin shirinku gani ya kori ji na jiya 21/12/2016 wanda kukayi waiwaye adon tafiya akan mahimmam abubuwan dasuka faru a shekarar 2016 mai daf da karewa, a gaskiya abubuwa masu yaws sun faru masu dadi da marasa dadi, amma data daga cikin mahimmam a gurina shine ziyarar zumunci da kuma bunkasa alaka da kut da kut wacce shugaba Muhammmadu Buhari na Nigeriya yakawo takaransa na kasar Sin wato shugaba Xi Jinping gaskiya wannan ziyara tayi armashi da samun nasara musammam ganin yadda aka kulla hulda tare kasuwanci ta $60 billion da gina alumma da samar da abubuwan more rayuwa na yau da kullum musammam layin dogo wanda zai hada sassa daban daban na Najeriya. Sannan akwanannan ziyarar mai girma gwamnan jahata ta Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Zuwa kasar Sin tare da hada huldar gina layin dogo da zai zagaya sassa na birnin Kano da kewaye wanda aikin zai lashe $1.8 billion biliyon na dallar Amurka agaskiya inda jahar datafi morar kasar Sin akan abubuwan more rayuwa da kasuwanci a Najeriya to jahata ta Kanon Dabo itace a farko. Akarshe inaiwa maaikatan sashen Hausa na CRI fatan alheri acikin sabuwar Shekara.

na gode. naku a kullum Abdulkadir Ibrahim Great Wall CRI Listeners Club Kano State Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China