in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yabo da jinjina ga ma'aikatan CRI musamman sashen hausa
2016-12-29 08:54:56 cri
Assalamu alaikum,

Ina mai matukar nuna farin cikina tare Da jin dadina da rubuto wannan wasika domin Yabo da jinjina ga dukkanin ma'aikatan CRI hausa domin jajircewa wajen sanar da masu sauraro irin wainar da ake toyawa a fadin duniya tun farkon shigowar sabuwar shekara ta 2016, inda muka soma da jawabin sabuwar shekara ta 2016 wanda shugaban Kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da kuma jawabin shugaban Gidan rediyon CRI baki daya suka yi jawabai masu ma'ana da amfani gaba su sauraron CRI a cikin dukkanin yaruka daban daban na duniya,

Ba shakka Gidan redio CRI ya zamo mai ki mai zagaya duniya da labarru da dumi duminsu tare da kwararrun ma'aikata a kowane fannin na cikin gida da ketare, a ko da yaushe mu masu sauraron muna gamsuwa da yadda suke aiwatar da aikinsu.

Muna jinjina ga ma'aikatan CRI hausa a kan kokarinsu musamma shugaban CRI hausa Malam Sanusi da malama Fatima Liu, da Lubabatu, Kande, Murtala, Bello, Ibrahim YAYA, Bilkisu, Saminu alhasan da dai sauransu.

Har wa yau ina jinjina ga Tsohon wakilin CRI hausa da ya zauna a birnin tarayya Abuja wato Malam Murtala da kuma tsohowar ma'aikaciyarku malama Fatima innuwa jibbirin da Kumar Malam Mamman Ada dukkaninsu aka kokarinsu na samar da ci gaban sashin Hausa na CRI a cikin shekara mai karewa ta 2016 da ma na baya da suka gabata. Ba shakka shekara ta 2016 tana kokarin wucewa tare da barin tarihi ga dukkanin mai sauraron CRI hausa baki daya ,

Daga karshe ina isar da godiyata ga dukkanin ma'aikatan sashen hausa na CRI a kan jan namijin kokarinsu wannan shekara mai karewa, fatarmu shekara ta 2017 ta fi Wanda ta gabata ameen nagode.

Bello Abubakar Malam Gero.

Kungiyr Masu sauraron Rediyon CRI.

Ta jihar sokoto.

Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China