in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kafa sabuwar bajinta a fannin yaki da talauci
2016-12-29 08:56:25 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga daukacin ma'aikatan sashen Hausa na CRI a Beijing, da fatan duk kuna cikin koshin lafiya.

Sanarwar hadin gwiwa da cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin tare da ofishin yaki da talauci da bunkasuwa na majalisar gudanarwa na kasar Sin suka fitar a jiya Talata 27, wacce ke bayani dangane da alkaluman dake nuna gagarumar nasarar da kasar Sin ta samu a fannin yaki da talauci na tsawon shekaru 30 ta yi matukar jan hankali na kuma ta burge ni.

Hakika, akwai ban mamaki da burgewa dangane da yadda alkaluman suka nuna cewa, kasar Sin ce ta lashe kashi 70 cikin 100 bisa kididdigar ayyukan yaki da fatara a duk fadin duniya. Wannan ya tabbatar da irin yadda kasar Sin ta tsaya tsayin daka ta yaki talauci da gaske cikin shekaru 30 lamarin da ya ba ta damar 'yanta al'ummar Sinawa kimanin miliyan 770 daga kangin talauci. Wannan ya nuna cewa mutanen da suka rage a cikin halin fatara a duk fadin kasar Sin basu fi miliyan 56 ba. Ba shakka, wannan abin a jinjina wa kasar ta Sin ne duba da cewa ita ce kasa mafi yawan al'umma kuma har ila yau, kasa mafi yawan al'ummar dake zaune a yankunan karkara tsakanin daukacin kasashen duniya.

A fannin muradan karni da MDD ta kaddamar tun shekara ta 2000, nan ma za a iya cewa kasar Sin ta ciri tuta bisa la'akari da cewa, kasar Sin ta cimma burin muradan karni na fatattakar talauci daga doron kasa, duba da cewa, ma fi rinjayen Sinawa sun tsallake mizanin talauci da MDD ta shata na gudanar da rayuwa sama da dalar Amurka 1.9 ga kowanne mutum a yini guda, kamar yadda alkaluman na cibiyar suka wassafa.

Bisa la'akari da wadannan alkaluma da kuma yawan al'ummar kasar Sin na fiye da biliyan daya da digo uku, amma duk da haka ta iya kafa bajinta a fannin yaki da talauci tsakanin daukacin kasashe masu tasowa, ya zama wajibi a cira wa kasar Sin hula. Ina fatan shugabannin kasashen mu na Afirka da talauci ya yi wa katutu za su yi koyi da irin salon kasar Sin kan yaki da fatara.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China