in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gurbacewar iska a arewacin China
2016-12-23 15:00:33 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya.

Tun bayan da birnin Beijing ya bayar da sanarwar gaggawa dangane da shiga yanayin gurbacewar iska mafi tsanani na farko a wannan shekara, wato sanarwa mai alamar launin JA a ranar Jumu'a 16, gurbatar iska ta ci gaba da fadada a arewacin kasar Sin, inda zuwa jiya Talata 20 ga wata adadin birane da suka ba da sanarwar gurbacewar iska sun karu zuwa 71. Lamarin da ya kawo tsaiko ga zirga zirgar ababen hawa, rufe makarantu da takaiata sauran harkoki da suka shafi kan hanya. Hakika, wannan lamari ya ja hankali na sosai sakamakon yadda na ke bayar da muhimmanci ga batun muhalli.

Kodayake, hukumomi a kasar Sin suna yin iya bakin kokarin su wajen daukan kwararan matakan shawo kan matsalar gurbacewar iska wacce ta addabi manyan birane da lardunan dake arewacin kasar, sakamakon yadda matsalar ke ci gaba da zama wata barazana ga lafiyar al'umma da sauran harkokin yau da kullum. Ko shakka babu, na gamsu da irin hobbasar da hukumomi a kasar Sin ke yi wajen yaki da matsalar gurbacewar iska musamman a yankin arewaci inda matsalar ta fi kamari.

Sai dai ga dukkan alamu, matsalar na neman zama gagara-badau, wato matsalar ta yi daidai da azancin nan dake cewa, ana maganin kaba kai na kara kumbura. A ra'ayi na, idan ana so a magance wannan matsala ta gurbacewar iska baki daya, to sai hukumomi sun yi kamar suna yi. Wato dole a bullo da hanyoyin da za su taimaka wa al'umma rage amfani da makamashin kwal, da rage yawan motoci dake kan hanya tare da fadada hanyoyin sufurin jiragen karkashin kasa, dai sauran sahihan matakai.

A karshe, ina fatan yanayin iska zai kara kyautata a arewacin kasar Sin kamar yadda ya kamata.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China