in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muna kewar barin aikin malam Mamman Ada da cri Hausa
2016-12-12 10:24:59 cri

A zamanin da yake aiki tare da cri Hausa, malam Mamman Ada bisa taimakon abokan aiki mamman Ada ya yi kokari sosai wajen kara mana wayin kai game da al'adun sinawa da kuma muhimman batutuwa da suka jibanci kasar Sin wayanda suka hada da muhimman guraren tarishi da yawan shakatawa da kuma manyan da kananan kabilun kasar Sin. Ba zan manta da ziyarar da mamman Ada a birnin Handan ba kana ba zan manta da irin gudumowa da Malam Mamman Ada ya bayar ga shirye-shiryen Allah daya gari Bambam tare da abokiyar aiki malama Lubabatu da kuma shirin Gani ya kori ji da dai sauransu. Babu shakka, malam Mamman Ada zai ci gaba da yin alfahari da kauna da karramawa da sinawa a cri Hausa da ma sauran sinawa abokai da aminai a kasar Sin suka nuna masa. Hakika mu masu sauraro, za mu dade muna kewar kammala aikin da Malam Mamman Ada ya yi da ku cri Hausa, domun muna jin dadin yadda yake gabatar da shirye-shirye a cri Hausa, masamman ma yadda yake magana tare da malama Lubabatu a cikin shirin Allah daya gari Bambam wanda shi da abokiyar aiki malama Lubabatu suke gabatar mana a duk mako.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban masu sauraron cri Hausa na jihar Yobe, taraiyar Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China