in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai sirri mai yawa tattare da wasan kung fu - Tai chi
2016-12-06 09:01:14 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku, da fatan duk kuna cikin koshin lafiya a birnin Beijing.

A yau Litinin 5 ga wata, na samu damar sauraron shirin ku na ' In ba ku ba gida' wanda malama Bilkisu Xin ta gabatar dangane da wata matashiyar Basiniya mai suna Chang Jia dake mallakar dakunan koyon wasan Kung fu - Tai chi har guda uku a birnin Shanghai.

Abin burgewa dangane da wannan matashiya Chang Jia shi ne, yayin da mafi rinjayen matasan Sinawa ke yin baya baya ga sha'anin al'adun gargajiya, ita kuwa ta mayar da hankalinta ne wajen bunkasa wasan kung fu Tai chi wanda Sinawa suka gada tun kaka da kakanni ta hanyar bude cibiyoyin koyar da wasan a birnin Shanghai, lamarin da ya ja hankalin baki 'yan kasashen ketare mazauna birnin na Shanghai da kuma Sinawa kimanin dubu 10.

Ba shakka, wannan shiri na yau ya ilimantar da ni sosai dangane da tasirin wasan kung fu Tai chi ta fuskar inganta lafiyar jiki da kuma koyon dabarun kare kai yayin fada. Hakika, akwai sirri mai yawa tattare da wannan wasa na kung fu Tai chi musamman yadda a ke daukan sa a matsayin wani nau'in motsa jiki da ya dace da tsofaffi.

A ra'ayi na, idan akwai matasa Sinawa masu sha'awar raya al'adun gargajiya irin Chang Jia da yawa, al'adun gargajiya da ke fuskantar barazanar bacewa za su samu tagomashi. A saboda haka, yana da muhimmanci gwamnati ta karfafa musu gwiwa ta hanyar ba su irin taimakon da suke bukata.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China