in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jinjinawa ga kasar Sin
2016-04-14 08:55:54 cri
Zuwa ga Fatima Liu sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa, dafatan kunanan lafiya.

Bayan haka inason yin amfani da wannan dama in jinjinawa kasar Sin akan bada lamini na US Six billion Dollars ga gwamnatin Najeriya a ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a kasar Sin lallai wannan ziyara tayi armashi sannan wannan kudade suna da mutukar amfani ga kasar Najeriya musammam a wannan lokaci wanda Najeriya tattalin arzikinta yana cikin wani mawuyacin hali inafatan wannan kudade za'ayi amfani dasu a guraren daya dace. Banda haka naji dadin hirar da kukayi da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai domin kun tattauna bayani masu mahimmamci akan yanayin da Najeriya take cikin a yau. Sannan ganawar shugaba Buhari da Zhang Dejiang tayi armashi sosai.

Ina muku fatan alheri.

Wassalam, Abdulkadir Ibrahim, G.C.L.C Kano.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China