in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Nuraddeen Ibrahim Adam a Kano
2016-04-09 11:40:34 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri gare ku, da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna nan lafiya a birnin Beijing.

Ina matukar farin ciki dangane da ziyarar shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari a kasar Sin, ziyarar da na ke fatan za ta kawo alfanu mai yawa ga bangarorin biyu. Kasar Sin ta riga ta samu ci gaba musamman ta fuskar kere kere da samar da ababen more rayuwa, a yayin da Nijeriya ta kasance wata babbar kasuwa da ke matukar bukatar kayayyaki na anfanin yau da kullum masu rangwamen farashi da kasar Sin ke samarwa. Wannan shi ne ginshikin hadin gwiwa da kara zurfafa dangantaka tsakanin Sin da Nijeriya.

Dangane da haka, ina fatan shawarwarin da shugabannin biyu Muhammad Buhari da Xi Jinping za su cimma a yayin wannan ziyara za su ba da fifiko ga batun taimaka wa Nijeriya samun wadatacciyar wutar lantarki, domin kasar Sin ta yi fice wajen fusahar samar da hasken lantarki ta hanyar amfani da hasken rana (solar) da ta hanyar amfani karfin iska wato (wind turbine). Hakika, a halin yanzu babbar matsalar da ke ci wa 'yan Nijeriya tuwo a kwarya bayan karancin man fetur, ita ce matsalar daukewar wutar lantarki akai akai.

A yayin da mu ke sa ran kara shigo da kaya kirar kasar Sin cikin Nijeriya, saboda yadda su ke da araha ga kuma inganci daidai gwargwado. Domin a zahiri kayayyaki kirar kasar Sin da ke da saukin farashi suna taimakawa kwarai wajen saukaka wa 'yan Nijeriya radadin rayuwa.

Da fatan wannan ziyara za ta bude wani sabon babin dangantaka tsakanin kasashen Sin da Nijeriya.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listener's Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China