in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin Hausawa a kasar Sin
2016-04-13 08:25:33 cri
A yau ranar Talata, 12 ga Afirilu, 2016, mun fara kallon wannan shiri na farko mai taken, 'Hauasawa a kasar Sin' a tashar NTA Hausa na Star times.

Adamu Muhammad Jajere da Kabiru Abbati Dankanti da Muhammad Salim Garba duk kan su Hausawa ne 'yan Najeriya, kuma dalibai a Jami'ar Koyon Kere-kere na Tianjin ta kasar Sin.

Shirin ya bamu damar sanin yadda rayuwarsu take a kasar Sin musamman a cikin azuzuwansu. Sannan shirin ya Kai mu har zuwa dakunan daliban da irin abincin da su kan ci. Har ma sun kai my zuwa wani daki wanda Jami"ar ta ware musu domin yin Ibadarsu da Salloli a ciki.

Zulaihat Muhammad da Maryam Aminu dalibai ne mata Hausawa daga Jihar Kaduna ta Najeriya, su ma mun kalle su zazzaune a cikin aji suna sauraren lacca da kuma karbar darussan koyon aikin aikin likita, tun da duk kan su dalibai ne a 'Jami'ar Koyon Aikin Likitanci na Tianjin. Sannan an nuna mana su a cikin dakin bincike da nazari a aikin likita. An fara kafa wannan Jami'a a shekara ta 1951. Abin yayi kyau sosai.

A gaskiya wannan shiri ya kayatar da ni, kuma na tabbata ya kayatar da wasu masu saurare da kallon wannan shiri. Sannan duk wanda ya kalli shirin zai amfana sosai domin akwai darussan rayuwa masu yawa a ciki, musammab ma ganin yadda wadannan dalibai suke harkokinsu na zamantakewa da karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali da tare da tsangwama ba.

Koda yake shirin bai yi tsawo sosai ba amma dai duk wanda ya kalla zai san an yi amfani da basira da tunani mai kyau wajen shiryawa, kuma dole a yaba. Kuma, Ina iya cewa, shirin ya Isar da sako mai nagarta da sanin yakamata.

Ina fata wannan shiri zai haifar da alheri, da kara dankon zumunci tsakanin al'ummomin kasashenmu baki daya. Wani abin farin ciki shine, galibin daliban da aka dauka a shirin suna karkashin daukar nauyin kasar Sin ne, watau 'scholarship scheme'.

A karshe, Ina fata wannan shiri da wadanda suka rage a baya zasu kara taimakawa wajen fahimtar juna ta fannoni da bangarori masu yawa.

Allah Ya taimakemu.

Naku,

Salisu Muhammad Dawanau

Abuja, Najeriya

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China