in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Shugaba Buhari kasar Sin
2016-04-12 09:06:31 cri
Assalamu alaikum,

Ina fata kuna lafiya. Allah Ya taimaka.

A yau, kusan duk kafofin yada labaran Najeriya suna da masaniyar wannan ziyara ta Shugaba Muhammad Buhari zuwa kasar Sin a ranakun 11 zuwa 15 ga Afirilu, kuma kowa na sane da kyakkyawar alaka dake tsakanin Sin da Najeriya.

A gaskiya, wannan ziyara ta zo a daidai lokacin da ta dace musamman domin yanzu ne ake so a kammala yarjejeniya a kan aikin jirgin kasa na Najeriya, sannan da wasu batutuwa masu muhimmanci na kara karfafa dankon zumunci dake tsakanin juna.

Muna fata za a yi nasara, sannan kuma kasashen namu zamu amfana da wannan ziyara. Muna kuma fata Shugaba Xi Jinping nan gaba shi ma zai kawo ziyara nan Najeriya.

Allah Ya taimaka.

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China