in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban taraiyar Nigeria Muhammadu Buhari a kasar Sin za ta zama ziyara mai cike da tarishi a huldar diplomasiyyar dake akwai a tsakanin kasashen 2
2016-04-12 09:05:03 cri

A ranar 14 ga watan February, 1971, kasashen Sin da taraiyar Nigeria suka kulla huldar jakadanci a tsakaninsu inda kawo yanzu kasashen 2 ke fara gudanar da shagulgulan bikin cikon shekaru 45 da kafuwar huldar diplomasiyya da cinikaiya da musayar al'adu da hadin gwiwa bisa man tsare-tsare da kuma sada zumunci a tsakaninsu. Dan haka, ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara yi a kasar Sin a ranar 11 ga watan mayu 2016, za zama ziyara mai cike da tarishi a huldar diplomasiyyar da kasashen 2 suka kulla zuwa wani saban mataki na ci gaba mai daurewa. Fatanmu shine, wannan muhimmiyar ziyara da shugaban taraiyar Nigeria Muhammadu Buhari zai fara yi a kasar Sin, za ta kara fadada huldar jakadanci a tsakanin kasashen Sin da taraiyar Nigeria kana ziyarar ta shugaban kasa Buhari a kasar Sin, za kara bude wasu sabbin shafukan yin hulda da juna a tsakanin kasashen 2 ta fannin kasuwanci, ilmi, musayar al'adu, yaki da ta'addanci, inganta harkokin aikin gona na zamani, zurfafa zumunci, hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da ritta hannu bisa manyan aiyuka da dai sauransu. Kana, muna fatan wannan ziyara za ta haifar da kyakkyawan sakamako mai nagarta tsakanin kasashen Sin da taraiyar Nigeria.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, taraiyar Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China