in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na ba da muhimmanci ga gidajen ajiye kayan tarihi
2014-03-26 09:29:33 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan dubun gaisuwa mai yawa da fatan alheri gare ku, ina fatan baki dayan ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na saurari sabon shirin 'Allah daya gari bamban' na jiya Jumu'a 21 ga wata, inda Malamai Lubabatu da Mamman Ada suka tattauna kan gidajen ajiye kayan tarihi na kasar Sin.

Ba shakka, na ji dadin sauararon wannan shiri domin ya kara bude min ido dangane da irin muhimmancin da kasar Sin ke dorawa kan adana kayan tarihi, musamman yadda alkaluman shekarar 2013 suka tabbatar da cewa akwai gidajen nuni tare adana kayan tarihi 3866 a kasar Sin. Hakika, wannan ya kai wani matsayi na koli a duniya, saboda ba na tsammani za a samu wata kasa a duniya dake da adadin gidajen ajiye kayan tarihi da ya kai wannan adadi. Amma a ra'ayi na wannan ba zai zama a wani abin ban mamaki ba, idan aka yi la'akari da cewa kasar Sin ta na da tarihin wayewar kai na kimanin shekaru 5000, tare da cewa har yanzu masu binciken kayan tarihi a kasar Sin ba su daina hakowa ko gano kayan tarihi da aka binne a karkashin kasa ba dubban shekaru da suka gabata.

Dangane da haka, ina ganin adadin gidajen ajiye kayan tarihin kasar Sin zai ci gaba da karuwa daga kan adadin da ake da shi a halin yanzu. Haka nan, idan aka yi la'akari da cewa, mahara na yammacin Turai da Amurka sun taba daka wawaso kan fadoji na daular Qing inda suka yi awon gaba da dimbin kayan tarihin da har yanzu ba a kai ga karbo su ba, hakika, a duk lokacin da kasar Sin ta cimma nasara karbo wadannan kayayyaki, game da wadanda ke hannun daidaikun Sinawa, to za a iya bude wasu sabbin gidajen kayan tarihi domin adana su. Wannan shi yake tabbatar da cewa, nan gaba gidajen ajiye kayan tarihin kasar Sin za su ci gaba da karuwa zuwa wani sabon matsayi na koli.

Godiya mai yawa ga hukumomin kasar Sin bisa habaka gidajen ajiye kayan tarihi, lamarin dake ba da haske mai yawa ga baki masu sha'awar al'adun Sinawa samun saukin fahimtar dogon tarihin kasar Sin, godiya ta musamman ga hukumomin na kasar Sin bisa samar da gidajen tarihi na kyauta wanda ba a biyan kudi fiye da 2500 a fadin kasar.

Mai sauraronku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ga wasu
v Allah daya gari bamban 2014-03-26 09:05:48
v Ziyarar uwar gidan shugaba Obama madam Michelle a kasar Sin 2014-03-21 17:40:37
v Sako daga mai sauraro 2014-03-19 14:23:09
v A gaishe ku da aiki 2014-03-18 09:59:17
v Sako daga mai sauraronmu Abdulkadir Ibrahim a Kano 2014-03-18 09:58:51
v Na saurari shirin 'Gani Ya Kori Ji' 2014-03-14 09:50:47
Ga wasu
v Allah daya gari bamban 2014-03-26 09:05:48
v Ziyarar uwar gidan shugaba Obama madam Michelle a kasar Sin 2014-03-21 17:40:37
v Sako daga mai sauraro 2014-03-19 14:23:09
v A gaishe ku da aiki 2014-03-18 09:59:17
v Sako daga mai sauraronmu Abdulkadir Ibrahim a Kano 2014-03-18 09:58:51
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China