Na rubuto cikin jin dadi da annashuwa don in nuna jin dadi na ga kasar Sin da Sinawa akan yadda a kullu yaumin suke wanke tunani da fadakar da jama'ar yankinmu na Afrika a kan yadda za su cire girman kai su samar wa jama'arsu ci gaba kamar yadda ita Sin din take yi ma 'yan kasata.
Wallahi ina magana ne a kan yadda gidan redionmu mai albarka ya kawo mana labarin gudanar da wani taron taimakawa kasashen Afrika wajen hasashen yanayi a nan kasar Sin a makon da ya gabata, inda aka gayyaci kwararru a fannin hasashen yanayi na kasashen Afrika guda 10, inda bayan horar da wadannan kwararru, gwamnatin Sin ta ce za ta taimaka ta samar da kudade, da fasahohi da kayayyaki gare su wajen hasashen yanayi, inda da wannan tallafi da kuma horo ne zaayi amfani a tinkari bala'u daga indallahi.
Wannan taimako da Sin ta yi ma Afrika ina gani kusan duk kasashen Afrika ciki har da kasata Najeriya ba wanda ke da tunanin yin haka. Allah ya saka ma Kasar Sin da mafificin Alhairi amin.
Ku kuma wannan gidan Rediyo wadanda kuke yi mana aiki dare da rana wajen kawo mana labarin yadda Sin take rayuwa da jamaa a duniya ba tare da bakin ciki ko cuta ba, illa don a sami cigaba a duniya Allah ya taimakeku, Allah ya kara daukaka ku Allah ya gwada mana ranar da Sin zata zama itace Babbar Uwa ga Kasashen duniya baki daya.
Daga karshe ina son ku isar da sakon gaisuwata ga babban yaya, Jarumin namiji a shugaban CRI Hausa Malam Sanusi Chen tare da 'yan uwa abokan aiki bisa irin jajircewar da suke yi a kullu yaumin wajen ganin sun fadakar da mu masu saurare.
Allah ya saka da alhairi, Mun gode
Mai sauraronku a kullum ta Internet da Digital Satelite
SANI SAMAILA MAFARA
ZAMFARA STATE
NIGERIA