Salaam. A ranar alhamis 20 ga watan March shekara ta 2014, uwar gidan shugaban Amurka Madam Michelle ta sauka a birnin Beijing na kasar Sin, domun amsa goran gaiyatar da uwar gidan mr. Xi Jinping madam Peng Liyuan ta yi mata. Madam Michelle Obama za ta kai ziyara a birnin Xi'an dake lardin shaanxi da kuma Chandu dake lardin Sichuan inda dabbar Panda mai alamun zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma mai dogon tarishin a kasar Sin. Wannan ziyara da Michelle ta kawo a kasar Sin inda za ta shafe kimanin mako guda, ta alamunta fadada dangantakar kasar Sin da Amurka na kara samun ci gaba a tsakanin kasashen 2 wato Sin da Amurka.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.