A ranar juma'a 21 ga watan 03/2014, na saurari shirin Alla daya Garin Bambam wanda malam Mamman Ada Da malama Lubabatu suka gabatar. Na ji dadin shirin a wannan rana, inda shirin ya yi tsokaci adangane da guraren adana kayan tarishi na gargajiya na kasar Sin. Abunda ya burge ni kuma ya bani mamaki shine, yawan guraren adana kayan tarihin gargajiya na kasar Sin ya kai kimanin 3366. To, wannan ya kara faiyace matsayin kasar Sin kasa daya tilo a dud duniya wajen yawan dadaddun muhimman guraren adana kayan tarishi masu ban sha'awa da kuma kara janyo hankulan masu yawan shakatawa da yawon bude idanu. Hakika magabatan kasar Sin sun yi matukar kokari wajen nuna kulawar masamman ga muhimman guraren adana kayan tarishi. Lalle kam, kasar Sin ta zama wata kasa a dud duniya da ta yi kaurin suna kuma ta yi zarra da fintinkau wa sauran kasashe takwarorinta.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.