in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga mai sauraronmu Abdulkadir Ibrahim a Kano
2014-03-18 09:58:51 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin ma'aikatanku suna cikin koshin lafiya.

Bayan haka a matsayina na ma'abocin kallon fina-finan Sinawa da son al'adunsu, lallai naji dadin karanta labaranku na facebook akan fina-finan da kasar Sin ke gabatarwa,lallai ni na karau sosai ta haryar kallon wannan fina-finai,ta sanin rayuwar Sinawa tare da tarihinsu. Ga wasu kadan daga fina-finar kasar dana kalla kuma nakeso. Crouching tiger hidden dragon, House of the flying tigers, Hero, 1911 revolution, The Founding of the People's Republic, Hero, Red Cliff 1,2, The curse of the golden flower, Wu Xie,Taichi 1, da sabo na 3D, the lost blade man, Assassin, Little dog soldier, the forbidden Kingdom, Painted Skin, Shanghai, Confucius, Mangol, Jumong, dadai sauransu. Inafatan CRI zasu dinga gabatar da bayanai akan fina-finan Sinawa.

Haka kuma naji dadin shirinku da kuka gabatar akan koyan yaren Sinanci ga 'yan kasashen waje. Lallai wannan shiri ya karawa masu sauraro kwarin gwiwa tare da jin dadi.

Inamuku fatan alheri.

Naku a kullum,

ABDULKADIR IBRAHIM,

GREAT WALL CRI LISTENERS CLUB,KANO.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China