Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, hakika na ji dadin sauraron shirin ku na 'Gani ya kori ji' na jiya Laraba 12 ga wata, inda Malamai Ibrahim Yaya, Saminu Alhassan da kuma Suwaiba Sulaiman Abdullahi suka tattauna tare da yin sharhi kan rufe taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.
Koda yake, daga cikin batutuwan da aka zartas yayin 'tarukan biyu' batun dokar kare muhalli ta fi jan hankali na. Saboda a zahirin gaskiya batun gurbatar iska a wasu manyan biranen kasar Sin ya ta'azzara, lamarin da ke barazana ga makomar lafiya da ma rayukan al'umma. Har ma na ji Sinawa mazauna birnin Beijing na tunanin barin birnin muddin yanayin iska a garin bai samu kyautatuwa ba. Haka ma lamarin yake ga wani mai yawon bude ido daga yammancin duniya, inda ya bayyana cewa, ko shakka babu gurbacewar iska a birnin Beijing za ta yi tasirin gaske wajen rage farin jinin birnin tare kore baki na gida da ketare dake ziyartar birnin a kowacce rana domin yawon shakatawa.
Sai dai kamar yadda Malamai suka tattauna, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na yaki da gurbatar iska sun burge ni, musamman baya ga rufe masana'antu dake amfani da makamashin kwal, hukumomin sun kuma tanadi wasu jiragen sama na musamman da za su rika sintiri a sararin samaniya suna zuke duk wata gurbatacciyar iska a duk lokacin da aka samu matsalar gurbacewar yanayi. Hakika, wannan labarin jiragen musamman ya burge ni, domin ban da cewa kasar Sin ce ta kirkiro wannan fusaha a karon farko a duk duniya, matakin ya kuma nuna cewa da gaske hukumonin suke wajen kawo karshen matsalar gurbacewar iska.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria