Ministan harkokin wajen Birtaniya, Jeremy Hunt, ya ce kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga bunkasar kasar Kenya da ma nahiyar Afirka baki daya, ta fuskar tattalin arziki da zaman takewar al'umma.
Mista Hunt ya bayyana haka ne a jiya, yayin taron manema labaru bayan ganawarsa da takwararsa ta Kenya, Monica Juma. Ya kara da cewa, kasarsa ta Birtaniya, ta yaba wa muhimiyar rawa da manyan ayyuka da kasar Sin ta yi, kamar layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, suka taka rawa wajen raya Kenya da ma nahiyar Afirka.
Mista Hunt da madam Juma sun nuna cewa, kasashensu za su kara inganta hadin gwiwarsu ta fuskar ciniki, da tsaron shiyya-shiyya da kiyaye muhalli.
Kenya, zango ne na karshe, na ziyarar da mista Hunt ya kai nahiyar Afirka a wannan karo. Kafin Kenya, mista Hunt ya ziyarci kasashen Senegal da Ghana da Nijeriya da Habasha.
Hanyar dogo tsakanin Mombasa da Nairobi ta zama wata alama ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya. Tun bayan watan Mayun shekarar 2017 da aka fara aiki da ita har zuwa yanzu, ta yi jigilar fasinjoji kimanin miliyan 2 da dubu 770 da kayayyakin da yawansu ya kai ton miliyan 4 da dubu 210, kuma matsakaicin yawan fasinjoji dake bin jirgin ya kai kashi 99 cikin dari. Hanyar dogon ta yi aiki yadda ya kamata ta fuskar tattalin arziki, har ta wuce zaton mutane. (Tasallah Yuan)