Jiya Talata 30 ga watan Afrilu ne wasu masana ilmin kimiyya matasa su 7 na kasar Afirka ta Kudu na rukunin farko, suka halarci bikin yin ban kwana da gida kafin tafiya kasar Sin, inda za su yi binciken hadin gwiwa, bikin ban kwanan dai ofishin jakadancin kasar Sin da ke Afirka ta Kudu, da ma'aikatar kimiyya da fasaha ta Afirka ta Kudu ne suka shirya shi a birnin Pretoria.
A yayin bikin, Lin Songtian, jakadan kasar Sin a Afirka ta Kudu ya karfafa gwiwar masanan ilmin kimiyya matasa na Afirka ta Kudu, yana mai fatan za su darajanta damar zuwa kasar Sin, inda za su yi koyi da juna a tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Sin, kana za su kara azama kan yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha da suke nazari a kai, tare da kara saninsu kan jama'ar Sin da tarihin Sin, a kokarin zama wakilin sada dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen 2.
Wani babban jami'in ma'aikatar kimiyya da fasaha ta Afirka ta Kudu, ya yi fatan zuwan masanan ilmin kimiyya matasa na kasar Sin kasar sa, a rabin karshen wannan shekara, inda za su yi bincike tare da takwarorinsu na Afirka ta Kudu. (Tasallah Yuan)