Farfesa Sheriff Ibrahim masanin harkokin siyasa da dangantakar kasa da kasa na Jami'ar Abuja dake Nijeriya ya bayyana cewa, kafa cibiyar muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen cimma muradun Sin da Afirka, lamarin da ya shaida cewa, Sin tana son kara fahimta da yin mu'amala a tsakaninta da kasashen Afirka.
Shugaban kungiyar hadin gwiwa da raya kasa kan hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da Sin ta kasar Morocco Nasser Busheba ya bayyana cewa, akwai bukatar yin nazari don kara inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ya yi imani cewa, cibiyar za ta taka muhimmiyar rawa wajen kara yin mu'amalar al'adu da ilmi a tsakanin Sin da kasashen Afirka, matakin da zai taimaka wajen inganta dangantakar dake tsakaninsu.
Babban sakataren watsa labaru na shugaban kasar Uganda Don Vanyama ya bayyana cewa, kwararrun masana kan harkokin Sin da Afirka a cibiyar. Za su taimaka ga zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da sada zumunta a tsakaninsu. A sakamakon hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni daban daban, kasar Uganda za ta kara samun moriya da fasahohi. (Zainab)