Kwanan baya, mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta Idai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu da haddasa asarar dukiyoyi a kasashen Mozambique, Zimbabwe da Malawi.
Yau Alhamis 21 ga wata, Tian Lin, kakakin hukumar raya hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya ya sanar da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta bai wadannan kasashe 3 taimakon jin kai cikin gaggawa domin taimaka musu yaki da bala'in, kana Sin tana son ba su taimako wajen sake gina kasa bayan aukuwar bala'in, gwarwadon karfinta bisa bukatun wadannan kasashe. (Tasallah Yuan)