Yau Laraba 20 ga wata, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana wa manema labaru cewa, sukar da aka yi kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka babu kamshin gaskiya a ciki. Kuma kasashen nahiyar ba su yarda da su ba.
Rahotanni na cewa, wasu kasashen yammacin duniya sun nuna shakku kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka bisa shawarar "ziri daya da hanya daya".
Yayin da Geng Shuang yake amsa tambayar manema labaru, ya nuna cewa, kasashen Sin da Afirka sun amince da juna. Akwai dankon zumunci a tsakaninsu, kana suna hada kansu a fannoni daban daban. Kasar Sin za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da kasashen Afirka a sassa daban daban bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" cikin sahihanci ba tare da rufa-rufa ba, a kokarin samun moriyar juna. Za su kuma aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2018 da kuma ra'ayoyin shugabannin Sin da Afirka suka cimma a yayin taron, a kokarin ci gaba da bunkasa huldar abokantaka da hadin gwiwa da ke tsakanin Sin da Afirka daga dukkan fannoni. (Tasallah Yuan)