in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lardin Zhejiang yana shirin kara kyautata alakar yawan bude ido da kasashen Afirka.
2019-03-06 20:37:43 cri
Darektan hukumar al'adu da yawon shakatawa na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin Chu Ziyu, ya bayyana cewa, lardinsa ya bullo da wani shirin shekaru biyar da zai yayata harkokin yawon shakara, inda za a tura matafiya 10,000 zuwa kasashen Afirka.

Chu Ziyu ya ce, Shirin zai taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa alaka tsakanin Sin da kasashen Afirka, haka kuma zai inganta fahimta tsakanin al'umomin kasashen biyu.

Yanzu haka dai, akwai kasashen Afirka da dama da suka sanya hannu kan wannan shirin, an kuma zabi kaashen Djibouti da Tanzaniya da Zimbabwe, a matsayin wuraren da baki masu yawon bude ido 300 da za su ziyarci Afirka a watan Mayu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China