Yau Litinin ne Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya musunta kalaman da Tibor Nagy, mai ba da taimako ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya yi dangane da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka.
Kakakin ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin na hada kai da kasashen Afirka cikin sahihanci ba tare da wata rufa-rufa ba, a kokarin neman moriyar juna. Yanzu Sin da Afirka na hada kai a sassa daban daban a nahiyar Afirka, lamarin da ya kawo wa jama'ar Afirka alheri a fannoni daban daban. Jama'ar Afirka su ne suka fi sanin ko wadannan matakan hadin gwiwa suna da fa'ida a gare su ko a'a. Ya kamata kusoshin Amurka su kara sauraren muryoyin jama'ar Afirka, su kara daukar matakan da suka dace a Afirka.
Kwanan baya, yayin da Tibor Nagy yake ziyara a kasar Uganda, ya ce, wai an yi zugugu ta sakamakon hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka. Amurka ta fi Sin ba da gudummawa a Afirka ta fuskar tsaro, amma a kan kyale shi. Filayen wasa da kasar Sin ta gina sun fi jawo hankalin 'yan Afirka, lamarin ya ba mutane haushi, in ji Tibor Nagy. (Tasallah Yuan)